Polaroid
Google69490f6862051cb8
google-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlgoogle-site-verification: google69490f6862051cb8.htmlBasheer journalist sharfadi14

Basheer journalist sharfadi14.jpg6
Basheer journalist sharfadi 11 1
Maraba Da Zuwa Wannan
Shafi Mai Al-barka 1

☀ Zabi inda kake son shiga ☀
Menunks
→Home
→Akidojin Ahlussunnah
→Addinin musulunci (35)
→40 Hadith (50)
→Fadakarwa (120)
→Neman labarai (20)
→Shi'a Kafirci (50)
→Hadith (55)
→Khudubobi (24)
→Tarihin magabata (60)
→Raddi / Maida martani (99)
→Face book post (30)
→Monthly Archives (60)
→Tambaya da Amsa (20)
→Sahabban Annabi {s.aw} (50)
→Taskar maluman sunnah (25)
→Akidar Y'an Shi'a Dangane da Al'kur'ani
→Fassarar Usulussunnah (20)
→Sheik Ja'afar {Rahimahullah} (65)
→Sheik Abubakar Gumi {Rahimahullah} (30)
→Sheik Dr. Muhammad Sani R/Lemo
→Salafiyyah Network Nigeria (100)
→Adam Sani Abu-Umayrah (99)
→Salaf Ustaz (79)
→Malama Ummi Ahmad Katsina
→Malama Amina Saleh Mande
→Labarai (40)
→Nishadantarwa (10)
→Siyasar Nigeria (9)
→Vidio (33)
→Audio (66)
→Hotuna (120)
→Internet Cheat (90)
→Site Achieve
→Application (10)
→Games (8)
→About me (01)

Wannan shafin mallakarCoollogo com-1281358 3
Ne




SHAFI DON KARUWAR MUSULMI
Tarihin magabata na kwarai daga littafin
Kaddara ta riga fata
Na
Sheik D.R Mansoor sokoto (Hafizahullah)
D
Shirinda y'ar uwarku
Malama Nabeelatu D Aliyu
Take GabatarwaKuna iya bin malama Nabeelah ta shafin face book
Wanda ya tsara ya kuma shirya
Basheer journalist sharfadi (Abu Hafsat)
A sha karatu lafiya

***TARIHIN MAGABATA NO 1***
.
.
ME YA FARU BAYAN MANZON ALLAH(SAW)?
.
Masu biye da wannan shiri nawa na (Tarihin Magabata Na Kwarai ) yau zamu shiga cikin Tarihin Khalifancin Sayyidina Abubakar Assidiq (RA ).
.
{Abubakar Na Manzon Allah}.
.
Sunan Abubakar Shine:-
.
Abdullahi Dan Usmanu dan Amiru dan Amru, dan Ka'abu dan Sa'adu dan Taimu dan Murratu.
.
Zumuncinsa da Manzon Allah (SAW ).
ya hadu ne a kakansa na shida "Murratu "wanda shi ma kaka ne na shida ga Manzon Allah (SAW ).
Ana yimasa lakabi da "Atiku ",ana kuma kiransa Abubakar, sannan ya shahara da "Siddiku ",sunan daya samu bayan da ya gaskata Manzon Allah (SAW )a lokacin da mutane suka karyata shi.
.
IYAYENSA:
.
Sunan Babansa Usmanu. Ana kuma yimasa Alkunya da Abu kuhafa.
.
Mahaifiyarsa: Sunanta Ummul khair, Salmah diyar Sakhr ita ma daga kabila daya ta fito da babansa, wato kabilar Banu Taim wadda karamar kabila ce kwarai idan Kwatanta ta da irin Banu Abdi munaf da Banu Mukhzum da sauransu.
.
Zan dakata anan sai lokaci na gaba, A madadin wanda ya sadani daku (Jamilu Ahmad Rimi ),Yar uwarku Nabeelatu D Aleeyu ke maku fatan Alkhairi.


***TARIHIN MAGABATA N0 2***
.
.
ABUBAKAR NA MANZON ALLAH.
.
Masu biye da wannan shiri na (TARIHIN MAGABATA NA KWARAI).
Inda muke jin Tarihin jan gwarzo sayyidina
Abubakar(RA).Daga littafin (KADDARA TA
RIGA FATA) Na (BABAN RAMLA ).
.
HAIHUWARSA: An haife shi a garin Makka
shekara ta hamsin da 1 kafin Hijra.Don
haka Manzon Allah (SAW)ya girme shi da
shekara 2 da watanni kadan.
.
SIFFOFINSA:
.
@Abubakar mutum ne fari, siriri, mai zurfin
ido, da babban goshi. Gashi kuma ya dan sunkuya kadan. sirintakarsa, wando baya
dauruwa da kyau a kugunsa.
.
DABI'UNSA DA HALAYENSA:
.
Abubakar (RA) ya kasance 1 daga cikin fitattun 'yan kasuwa masu fatauci. An bayyana shi da halin kirki fice da kyauta.Kuraishawa na darajanta shi saboda dattakunsa da karamcinsa.
.
Yana daga cikin abin dake bayyana kaifin hankalinsa, haramtawa kansa shan giya da
yayi shida abokinsa Usmanu dan Affan. Ba wanda ya taba kurba ta daga cikinsu tun
kafin bayyanar Musulunci.
.
An bada labarin cewa, tun asali Abubakar ya haramta wa kansa shan giya ne saboda yaga wani mutum da ya bugu da ita yana
sanya hannunsa a cikin najasa ya kuma nufi bakinsa, kana idan yaji wari sai ya janye hannunsa daga bakin.
.
Daga nan ne Abubakar ya kyamace ta har yayi rantsuwa
ba zai sha ta ba.
.
Haka ma bai taba bautar gumaka ba domin da Allah ya nufi kawar dashi daga wannan sai mahaifinsa yaje dashi yana yaro ya kai shi a wurin gumaka ya sanar dashi cewa, ga iyayen gijinsa nan wadanda ake bauta, ya tafi ya bar shi nan. Shi kuma Abubakar daya ji yunwa sai ya roke su abinci bai ji sun ce masa uffan ba, ya roke su ruwa basu ce masa ci kanka ba.Daga nan ya tofa masu
yawu, ya zage su ,yayi tafiyarsa yana mai tsananin kyamarsu da kaurace masu.
.
Haka ma Abubakar bai iya waka ba. Ba za muyi mamakin wadannan dabi'un na Siddiku
ba sanin cewa,shi babban ability ne, masoyi ga shugabanmu (SAW) tun zamanin kuruciya har manyanci. Mutum na kirki kuwa daga abokinshi ake ganewa .
.
ANAN ZAN DAKATA SAI LOKACI NA GABA.
.
Amadadin wacce ta sadani daku (HAFSAT AHMAD UMMI ),Ni yar uwarku a musulunci
(Nabeelatu D Aleeyu ) nake cewa Allah yakara mana kaunar fiyayyen Halitta da
dukkan Sahabbai.


***TARIHIN MAGABATA N0 3***
.
.
ME YA FARU BAYAN MANZON ALLAH (SAW )?
.
Masu biye da wannan shirin (Tarihin Magabata Na kwarai) muna cikin Tarihin Sayyidina Abubakar (RA) Shirin zai cigaba yanzu.
,
IYALINSA:
.
Abubakar RA ya auri mata 2 kafin musulunci, 2 bayan musulunci. Matansa na farko sun hada da:
.
1-Kutailah diyar Abdul Uzzah, wadda ta haifi masa Abdullahi da Asma'u.
.
2-Ummu Rumana diyar Amir 'yan Kabilar Kinanata,wadda ta haifa masa Abdul Rahman da uwar Mumunai A'ishatu.
.
Matansa na daga bisani kuwa sun hada da:
.
3-Asma'u Diyar Umais, wadda ta fara auren Ja'afar Dan Abu Dalib. A bayan rasuwar Abubakar kuma ta auri Ali Dan Abu Dalib. A kowane gida daga gidajen 3 datayi aure ta haifi Muhammad.
,
4- Habibah diyar Kharijah daga cikin Ansaru (Mutanen Madina),ya rasu ya bar ta da cikin Autansa Ummu Kulsum.
.
Zan dakata anan ku biyoni gobe da yardar Allah don ganin cigaban shiri.
.
Yar uwarku A musulunci Nabeeelatu D Aleeyu.


***TARIHIN MAGABATA N0 4***
.
MEYA FARU BAYAN MANZON ALLAH (SAW) ?
.
Masu biye da wannan shiri na {Tarihin Magaba na Kwarai) Gani dauke da cigaban shirin.
.
Idan baku manta ba muna cikin (Khalifancin Abubakar Dan Abu Kuhafa R.A).
.
MATSAYINSA KAFIN ZUWAN MUSULUNCI.
.
Abubakar yayi fice a zamanin Jahiliyya da ilimin da ake kira Ansab,sanin dangantakar mutane da Tarihin gidajensu da abubuwan Arziki ko rashin arzikin da suka gudana a tsakanin mutane ko a tsakanin Kabilu.Sannan kuma shi ne wakilin reshen gidansu a majlisar ZaRtarwa ta Kuraishawa wadda ta hada rassa goma na wannan Kabilar, ko wane gida yana da aikinsa da wanda yake wakiltarsa.
.
Ga su kamar haka:
.
1-Banu Hashim: Su ke kula da shayar da Alhazzai ruwa. Wakilinsu a majlisa shine Abbas dan Abdul Muddalib.
.
2-Banu Umayyah: Su ke rike da tutar Kuraishawa, kuma suke rokon kwarya duk lokacin da aka rasa shugaba kafin a hadu akan sabon da za a hada. Wakilinsu a Majlisa shi ne Abu Sufyan dan Harb.
.
3-Banu Naufal:su ke kula da asusun tallafi na taimakon Alhazan da guzuri ya yanke masu. Wakilinsu shi ne Al Haris dan Amir.
.
4-Banu Abdid Dar: Su ke kula da wanke ka'aba da tufatarwa.
.
5-Banu Asad: Suke da ofishin sakatariya. Duk shawarar da aka yanke suke sa mata hannu kafin a aiwatar da ita. Wakilinsu shine Yazid dan dan Zam'ah dan Aswad.
.
6-Banu Taim: Su ke da Alhakin hada kudi don biyan diyya, Wakilinsu shine Abubakar dan Abu khuhafa.
.
7-Banu Makhzum: suke kula da wurin ajiyar kayan yaki, wakilinsu shine Khalid Dan walid.
.
8-Banu Adiyyan: Sune masu kula da huldar kuraishawa da sauran Kabilu, musamman a wajen sha'anin yaki da zaman lafia. Wakilinsu shine Umar dan Khattab.
.
9-Banu Jumah: Su ke kula da Kuri'ar da ake yi don neman sa'a in za ayi tafia ko ciniki ko aure ko makamancinsu.
.
10-Banu Sahm: su ke kula da tattalin arzikin da abinda ya shafi gumaka. Wakilinsu shine Al Haris dan Kais.
.
Anan zan tsaya, sai mun hadu a lokaci na gaba.Amadadin wacce ta sadani daku {Hafsat Ahmad Ummi },
.
Nida na gabatar yar uwarku A musulunci Nabeelatu D Aleeyu.


***TARIHIN MAGABATA N0 5***
.
.
KADAN DAGA CIKIN DARAJOJIN ABUBAKAR SIDDIQ (R.A)
.
Shine farkon wanda yafara
musulunta a cikin maza
.
2.Shine ake Rubuta
sunansa bayan sunan
manzon Allah (s.a.w),
.
3.Shine shugaban musulmai bayan manzon Allah,
.
4. Shine yake kwana
yana ibadah,
.
5. Shine zaizo ranar kiyamah,
yana amintacce,
.
6. Shine yake ciyar da dukiyar
sa duka,
.
7. Shine majidadin annabi,,
.
8. Mai gudun duniya, mai kwadayin lahira,,
.
9. Allah yayarda dashi,,
.
10. Mai tsananin tsoron
Allah,,
.;
11. Mai gaskiya, kuma mai gaskatawa,,
.
12. Mafificin Halitta bayan Annabawa da manzanni,,
.
13. Farkon masoyin manzon Allah(s.a.w),,
.
14. Farkon wanda zai fara
shiga Aljannah, bayan Annabawa, da manzanni,,
.
15. Farknn wanda za fara shiga Aljannah a cikin Al'ummar Annabi,,
.
16. Dattijon muhajirai, da Ansar,,
.
17. Farkon Dalibi a makarantar
manzon Allah (s.a.w),
.
18.Shine idan yaji Alkur'ani yake
kuka,,
.
19. Shine Siddeeq,,
.
20. Shine wanda aka 'yantashi
daga wuta
.
wannan shine Abubakar siddeq,
Allah yakara masa yarda.

***TARIHIN MAGABATA NA KWARAI no: 6.***
.
(MUSULUNTAR SAYYIDINA ABUBAKAR RA).
.
Masana Tarihi sun ruwaito cewa,tun kafin wahayi ya fara sauka ga manzon Allah (SAW) Abubakar yayi wani mafarki wanda ya labarta shi ga malamin nan masanin Addinin Nasara da ake ce ma Bahirah.Sai ya tambaye shi daga ina ka fito? Yace masa ,Bakuraishe.Ya ce mene ne sana'arka? Yace, Fatauci. Bahira yace idan ALLAH ya gaskata mafarkinka to, wani Manzo zai bayyana daga cikin jama'arka, za ka taimaka masa a rayuwarsa ,kuma ka wakilce shi bayan mutuwarsa.
.
A wata tafiya kuma da yayi zuwa kasar yaman ya samu bushara mai kama da wannan daga wurin wani malami daga Kabilar Azd.
.
A lokacin da Allah madaukakin sarki ya Aiko Manzonsa, Abubakar baiyi wata wata ba ya gaskata shi yana mai cewa, bamu taba gwada karya a kanka ba, kuma ka cancanci manzanci saboda tsoron amanarka da sada zumuncinka da kyakkyawar zamantakewarka da jama'a.
.
Daga nan kuma Abubakar yaci gaba da zama na hannun daman Manzon Allah Sallalahu Alaihir Wasallama har in da mai raba masoya ta raba su.
.
Zan dakata anan sai lokaci na gaba,Amadadin wacce ta sadani daku (Hafsat Ahmad Ummi )Ni dana shirya na kuma gabatar nake cewa Allah yakara mana kaunar Manzon Rahma tare da Sahabbansa.


[TARIHIN MAGABATA NA KWARAI ].NO: 7.
.
ABUBAKAR NA MANZON ALLAH (SAW).
MASU biye damu acikin wannan shiri nawa na
[TARIHIN MAGABATA NA KWARAI ].
.
Yanzu Shirin zai cigaba.
Gudunmuwarsa Ga Addini:
Kasancewarsa mutum mai Arziki, dattijo, kuma na hannun damar Manzon Allah (SAW )ya bashi damar taimaka ma Addinin Musulunci ta hanyoyi da dama;
.
A makka ya kasance mai bada kariya ga Manzon Allah (SAW )daga musgunawa da cin zarafin da mushrikai su ke masa.
.
Har ma Ali Dan Abu Dalib yake cewa, bayan mutuwar Abu Dalib babu wanda yake cema kafiri kanzil idan suna musgunawa Manzon Allah sai Abubakar. Ga kuma dukiyarsa da yayi amfani da ita wajen cigaban addini har ma manzon Allah (SAW )da kansa yake cewa,
.
"Dukiya kowa bata amfane ni ba kamar yadda dukiyar Abubakar ta amfane ni ".
.
Abubakar ya taya Manzon Allah (SAW ) wajen kiran mutane zuwa ga Musulunci inda ya janyo musuluntar kusan dukkan Mukarrabansa da Amintattunsa kamar su Usmanu dan Affan da Zubairu dan Awwam da Dalhatu dan Ubaidallah da Abdur Rahman dan Aufu da Sa'adu dan Wakkas wadanda dukkansu suna cikin mutane 10 da Manzon Allah (SAW ) yayi wa bushara da Aljannah.
.
Sannan daga bisani ya musuluntar da Usmanu dan Maz'un da Amiru (Abu Ubaidah )dan jarrah da Arkamu dan Abul Arkam da Abu Salamata Al Makhzumi wadanda su ne magabatan farko a shiga Musulunci.
.
ALLAHU AKHBAR!
.
Amadadin wacce ta sadani daku
(HAFSAT AHMAD UMMI) YAR UWARKU A MUSULUNCI ~Nabeelatu D Aleeyu, nake cewa mu hadu a sati mai zuwa.


[5:00pm, 11/30/2014]
.
Nabeelerh: Assalamu Alaikum,
.
Masu biye damu acikin wannan gida mai Albarka, barkanmu da sake saduwa acikin cigaban shirin.TARIHIN MAGABATA NA KWARAI N0 8. KADA DAI A MANTA HAR YANZU MUNA NAN NE ACIKIN TARIHIN SAYYIDINA ABUBAKAR NA MANZON ALLAH SAW,
.
SHIRIN ZAI DORA YANZU.
.
WASU DAGA CIKIN DARAJOJINSA.Babu wani daga cikin Sahabban Manzon Allah SAW wanda ya tara darajoji, musamman wadanda yakebenta dasu kamar Abubakar.
.
Daga cikin darajojinsa akwai tsananin kusancinsa ga Manzon Allah SAW da kasancewarsa Abokin sirrinsa. Misali shi kadai ne wanda Manzon Allah SAW ya sanar dashi yana son Hafsah kafin yayi maganar aurenta.
.
Ga kuma ayoyin Alkur'ani da suka sauka suna yaba ma halayensa na jarunta da karamci da tsoron Allah.
.
Ga kuma fifikonsa na ilimi a kan sauran Sahabbai, domin dukkansu sun aminta cewa, bayan dai ya kebanta da sanin ilimin nasaba (Dangatakar mutane da sanin Tarihin kakanninsu)kuma shi ne yafi su ilimi daga manzon Allah SAW.
.
Manzon Allah SAW yayi mafarkin an kawo masa madara a cikin wata kwarya sai ya sha har ta gudana a tsakanin fatarsa da tsokarsa, sannan sai ya baiwa Abubakar. Sahabbai suka fassara wannan da cewa, ilimin da Allah yabashi ne ya rage wa Abubakar. Sai Manzon Allah SAW yace kunyi daidai! Kun yi daidai!!
.
Abubakar kuma shine ne mafi tsentseni da tsoron Allah Allah a cikinsu.Sbd tsentseninsa ne ya taba amayar da madarar daya sha domin yayi shakkar halalcinta.
.
Haka kuma Manzon Allah SAW ya bashi shedar Tawali'u da rashin girman kai alokacin da ya ce masa, kai ba ka jan wandonka saboda girman kai.Imaninsa kuwa ya rinjayi na sauran jama'a kamar yadda Manzon Allah SAW ya bayyana a wurare da dama.
.
Shi kadai ne yake fatawa a gaban manzon Allah SAW, shi kuma kadai ne yake wakiltarsa a abinda ya kebance shi kamar limancin sallah da jagorancin Hajji da makamantansu.
.
Zan dakata anan sai lokaci na gaba idan Allah ya yarda,
.
A madadin wacce ta sadani daku (Hafsat Ahmad Ummi) ni Nabeelatu D Aleeyu ke maku fatan Alkhairi.


[6:18pm, 12/4/2014]
.
Nabeelerh: ASSALAM ALAIKUM
BARKANMU DA SADUWA A CIGABAN TARIHIN MAGABATA NA KWARAI NO 9.
.
JURUMTAKARSA DA TSAYUWAR RA'AYINSA.
.
Da yawan marubutan tarihi suna kallon Abubakar a matsayin mutum mai rauni, maras kuzari,wanda sanyin halinsa ya rinjayi karfin jikinsa.Sukan dauki Umar a matsayin karkarfa, matsannanci mai kazar kazar.
.
Wannan sai yasa mafi yawan makaranta suka kuskuri fahimtar wane irin mutum ne shi Abubakar.
Ga wasu daga misalai a gurguje da zasu wargaza wannan gurguwar fahimta nan take:
.
An tambayi Sayyiduna Ali R.A wanene duk yafi jarumta?sai yace, ba shakka ni ban taba fito na fito da Namiji ba sai na kada shi,
.
Amma a cikinmu jarumi shine Abubakar. Sai Ali ya bada labarin irin bajintar Abubakar a ranar da akayi yakin Badar wanda shine karo na farko da musulmai suka fara sanin yaki.
.
Ba dai wani wani yaki da Manzon Allah SAW ya fita ba ba tare da Abubakar yana tare dashi ba.ya kuma shugabartar dashi akan rundunar yaki bau 1 ba.
.
Kuma ba inda yaje ba tare da Allah yabasa Nasara ba.
.
Misali a shekara ta bakwai bayan Hijra shi ya shugabanci rundunar data yaki Banu Fizarah ya ganimanto dukiyarsu.
.
sannan shi yake rike da tuta a yakin da yafi kowane tsananta a kan musulmi,shine yakin Tabuka. A ranar yakin Hunaini kuwa musulmi sun sha wahalar data sa akasarinsu suka ja da baya kamar yadda Allah yafada a Aya ta (20) acikin (SURATUL ALI IMRAN).
.
Amma duk da haka Abubakar ya tsaya wurin manzon Allah SAW,yana bashi kariya tare da yan kadan daga cikin Sahabbai wadanda suka hada da UMAR da ALI da Fadlu dan Abbas da Babansa Abbas da Usamatu da Abu Sufyan dan Harisu.
.
To wane irin kuzari muke nema ga wanda yake a duk yake-yake shine yake tare da jagoran tafiyar SALLALLAHU ALAIHI WASSALAMA?
Wannan shine Raggo? A dai sake Nazari!
.
Zan dakata anan, sai lokaci na gama idan rayuwarmu yakai.
.
A madadin (Hafsat Ahmad Ummi) data sadani daku,
.
Ni yar uwarku a musulunci Nabeelatu D Aleeyu nake mana fatan mutuwa da soyayyar Sahabban Annabi A zukatanmu.


**TARIHIN MAGABATA N0:10**

ASSALAMU ALAIKUM,
Kamar yadda kuka sani munan acikin Tarihin Sayyiduna Abubakar na Manzon Allah.
Shirin da Nake kawo muku a duk sati Yanzu shirin zai cigaba.

NUNI YA ISHI MAI HANKALI.

Tun kafin cikawarsa Manzon Allah SAW ya bayyana ma musulmi sha'awarsa ga khalifantar da Abubakar a madadinsa.Ga shi dai shine Amirul Hajji guda 1 da aka tabayi a zamanin Manzon Allah SAW,ga kuma shi an umurce shi da bada sallah.

Wasu mutane kuma sun nemi Manzon Allah SAW ya fada musu inda zasu kai zakkarsu a bayan rayuwarsa sai yace, su kai ma Abubakar.

A yayin da yayi ma wata Mace hukunci kuwa ya ce mata,ki dawo lokaci kaza,sai tace,to in ban tarar da kai bafa? Tana nufin in rai yayi halinsa. Sai Annabi SAW yace mata,sai kije ki samu Abubakar.

To in ko har yakasance Abubakar shi zai jagoranci sallah da Hajji da sha'anin zakkah kuma ya yanke hukunci a tsakanin mutane to ina wani shugaba ba shi ba?

Wani lokacin ma Manzon Allah SAW yakanyi umurni da akira masa Abubakar da iyalansa don ya bada wasicci gare su amma kuma sai ya fasa yana mai karawa da cewa Allah bazai bari a kaucewa Abubakar ba,musulmi ma kuma baza suyi hakan ba.

Lokaci na karshe da hakan yafaru shine a daren Juma'arsa ta karshe a duniya inda Manzon Allah SAW yace a kawo masa takarda zaisa a rubuta alkawari Wanda zai hana sabani amma sai sayyiduna Umar yace:-

'' kar Ku matsa ma Manzon Allah,ga littafin Allah a gabanmu ,me kuke nema daga Manzon Allah SAW ? Ai zafin ciwon da yake fama dashi ya ishe shi''

Da aka soma maganganu akai sai Manzon Allah SAW yace :

"Ku tashi Ku tashi Ku bani wuri!"

Bai kuma sake wannan maganar ba a sauran wuni hudu da yayi bayan haka a duniya.

ABUBAKAR YA ZAMA KHALIFAN FARKO:

Ba zai yiyu ga duk wata al'umma mai cin gashin kanta ba ta wayi gari kuma ta maraita ba wani shugaba akanta.

Wannan shi zai fassara irin hanzarin da aka yi wajen tsayar da Wanda zai gadi Manzon Rahma SAW.

A yammacin ranar littinin ne wadda Manzon Allah SAW ya cika a cikinta, Abubakar ya samu labarin cewa,Ansaru, mutanen Madina sun yi gangami a wajen da ake kira SAKIFA, can arewancin birnin sun fara Nazarin sha'anin khalifanci a bayan Manzon Allah SAW.

Kai tsaye Abubakar ya tasamar wurin wannan taron na Ansar domin ya gane ma idonsa irin wainar da ake toyawa.
A tare dashi akwai mutane 2 daga cikin manyan Muhajirai,sune;

1, Umar Dan Khaddabi,
2, Amiru (Abu Ubaidata)
dan Jarrah,

Wadanda bisa ga Sa'a ne suka hadu dasu da batare da an je nemansu don su halarci taron ba.

Da Abubakar ya iso wurin taron sai ya nemi su gabatar masa da bayanin abinda suke ciki. Magabata daga cikinsu sukayi jawabai cike da yabawa ga kawunansu da bayyana irin matsayinsu a musulunci.Umar yaso a bashi dama bayan haka yayi magana,amma Abubakar ya nemeshi daya dakata. Sannan shi Abubakar din yayi wani gajeren jawabi Wanda ya tabbatar ma Ansaru da duk abinda suka fadi na falala har ma da kari akan hakan. Ya kara da cewa : amma kuma kun sani mutane bazasu iya mika wuya ga wata kabilar ba saita kuraishawa.Wannan shi yasa ManZon Allah SAW yabada umurnin tsayar da manyan shugabannin Ansar, Sa'adu Dan Ubaida (Wanda shine Ansar sukeso su Nada a matsayin Khalifa) cewa,ko kaji wannan bayani daga Manzon Allah SAW,Sa'adu yace eh.

Ganin haka ta faru,ga gaskiya ta fito filing cewa, akwai Matsala wani ba bakuraishe ba ya jibinci wannan lamari, kuma ga umurnin Manzon Allah SAW Wanda shugaban nasu yayi ikirari a kansa, sai jikinsu yayi sanyi,ya kasance ba abinda ya rage a Kansu sai mika wuya ga gaskiya.

Don haka nan take Abubakar yace masu, to in haka ne,ni na aminta Ku Nada dayan wadannan buyun dake tare dani Umar ko Abu Ubaidah domin ko wannensu ya cancanta.

Fadin haka da Abubakar yayi sai wani daga Ansaru yace, ni na Samar maku da wata mafita mai sauki itace,a nada shugabanni 2, daya daga cikinku daya daga cikinmu. Sai Zaidu Dan sabitu (daya daga cikin Ansaru din har wayau) yace a'a gaskiya dai ita CE,Manzon Allah SAW shine ya kasance shugaba,mu kuma mune mataimakansa. Don haka, su nada khalifa mu kuma mu taimaka masa. Anan ne Umar yayi wata magana wadda ta dada kashe masu jiki baki daya. Ya ce, yaku jama'a! Manzon Allah SAW fa shine ya nada Abubakar don yabamu sallah. Acikinmu wannene yake iya mayar dashi baya shi ya shiga gaba?

Da haka dai Umar ya nemi amincewar Abubakar don yayi masa mubaya'a. Nan take kuma sauran jama'a gaba daya suka Mara masa baya batare da wata jayayya da ta biyo bayan hakan ba. Washegari ranar talata Abubakar ya Zauna akan mimbari sauran al'umma suyi tasu mubaya'ar musamman Muhajirai da aka yi wancan taron ba da su ba.

Alhamdulillahi anan zan dakata sai Lokaci na gaba,
Yar uwarku (Nabeelatu D Aleeyu) ke cewa mu zama lafiya)


koma saman shafi

→Labarai
1234...9899100»

Share|

Kaima shiga a tattauna da kai
* No boards.

Online: Guests: 1


→Ra'ayin jama'a game damu

 IDAN KANA BUKATAR A TALLATA MAKA HAJAR KA A WANNAN SHAFIN DA SAURAN SHAFUKAN MU KANA IYA TUNTUBAR MU TA WADANNAN HANYOYIN KAMAR HAKA:


Email: bjournalist55@hotmail.com

Phone No: 09035830253

Facebook: Basheer Journalist Sharfadi

Address: Ittihad Computer Centre,  No 92 Daneji Kano


MAI TALLA SHI KE DA RIBA


*Bayanan ka*
Browser din da ka hawo Mozilla

Kasar da kake

Adadin Maziyarta 345296

Adadin Wadanda Sukayi Comment 65691

A Wadanda Suka Shiga Tattaunawar Mu 54


Follow @bjournalist55
→Yi Adding Dina Ta Facebook
→Yi Like Na Dakarun Sunnah Page
→Yi Like Dina Ta Facebook

*Shafuka Masu Alaka Da Mu*

→Basheer Sharfadi wordpress
Basheer Sharfadi Blog Spot
UP
→Home

Basheer Journalist Sharfadi (Abu Hafsah)
ISLAMIC DATE
  • phpimg2.php?it&ic=yellow



  • Click to Sms
    Click to Call


    Basheer journalist sharfadi3
    Coollogo com-1281358